Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Bayan shafe shekaru 78 da mamayar Falasdinu a hannun Sahayoniyawa, Isra’ila na ci gaba da tilastawa Faladinawa yin ƙaura ta hanyar rushe gidaje da kwashe dukiyoyinsu, da fadada gina kananan garuruwa domin samarwa da Isra’ilawa wuraren zama, wanda hakan ya shafi rayuwar miliyoyin mutane a Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza.
Bisa ga sanarwar Hukumar Kididdiga, yawan Falasdinawa a cikin ƙasar Falasdinu a yanzu ya kai miliyan 5.6, wanda ya haɗa da miliyan 3.43 a Yammacin Kogin Jordan da miliyan 2.13 a Zirin Gaza. Haka nan, kusan mutane miliyan biyu a Gaza da kusan 40,000 a arewacin Yammacin Kogin Jordan an tilasta musu yin ƙaura saboda ci gaba da cin zarafi da keta iyakar da Isra’ila ke yi aiwatarwa ba tare da iyaka ba.
Dangane da haka Ziyad Abihis, masanin harkokin Kudus, ya yi gargadin cewa Juma'a mai zuwa na iya zama Juma'a mafi hatsari ga Masallacin Al-Aqsa tun daga lokacin da aka mamaye shi; musamman a inuwar tsare-tsare da ƙungiyoyin Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi ke bi tare da haɗin gwiwar gwamnati da 'yan sandan gwamnatin Sahayoniya don tabbatar da sabbin abubuwa a Masallacin Al-Aqsa.
………………………………………………….
Your Comment